//
Wednesday, April 1

Gwamnatin jihar Kano ta dawo da dokar hana cakudar Maza da Mata a baburan ‘Adaidata Sahu’

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Gwamnan jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana shirin gwamnatin jihar na hana cakuduwar Maza da Mata a babur ‘Adaidata Sahu.’

Gwamnan ya bayyana cewa daga 1 ga watan sabuwar shekarar 2020, dokar zata cigaba da aiki.

Haka zalika, DABO FM ta rawaito cewa; Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta sabunta dokar hana cakuda maza da mata a cikin baburin Adaidaita Sahu.

Hukumar ta bukaci gamayyar kungiyoyin direbobin mashin mai kafa uku (A daidaita Sahu) da su guji ci gaba da cakuda Maza da Mata wajen gudanar da haya a ababen hawansu daga 1 ga watan Janairun sabuwar Shekarar 2020 mai kamawa.

Dabo FM ta tattaro babban Kwamandan Hisbah na jihar Kano, Shaikh Harun Muhammad Sani Ibn Sina, yana bayyana hakan a lokacin da yake ganawa da gamayyar kungiyar direbobin baburan masu kafa 3 na Adaidaita Sahu.

Masu Alaƙa  Manyan bukatu 5 da Ganduje yake so majalisa ta zartar masa kan masarautar Kano

Wanda hukumar ta gayyato su domin sanar da su cewa an sabunta dokar nan da ta yi hani da cakuda Maza da Mata a cikin Ababen hawa, Kuma za ta fara aiki daga ranar 1 ga watan sabuwar shekara mai kamawa.

Shaikh Ibn Sina ya bayyana cewa “An samar da wannan doka ne tun cikin shekara ta 2002, kawai dai an sake sabunta ta ne don ganin an tabbatar da babban aikin hukumar Hisbah na Umarni da kyakkyawa da kuma hani ga mummuna.”

Ya kara da cewa “Kasantuwar yadda aka yi watsi da bin wannan doka, wanda kuma hakan ba karamar fitina yake haifarwa a cikin al’umma ba.”

Masu Alaƙa  Yau watan Yuli yake 35 a jihar Kano - Ma'aikata a jihar sun koka bisa rashin Albashi

Kwamandan na Hisbah ya ce “Daga wannan rana da aka ambata, dakarun Hukumar za su fito domin su tabbatar da cewa an bi wannan doka sau da kafa.”

“Inda a matakin farko za a fara da yin nasiha, sannan kuma sai biyan tarar kudin da ba su gaza N5,000 ba ga duk wanda aka samu da laifin bijirewa wannan doka.”

A nashi jawabin Shugaban gamayyar kungiyoyin direbobin Mashin mai kafa uku na jihar Kano, ya bayyana cewar za su sanar da dukkan mambobinsu game da wannan doka, kuma a matsayin su na Musulmi suna goyon bayanta kuma za su bada dukkan hadin kan da ake bukata.

Karin Labarai

Share.

About Author

Comments are closed.

%d bloggers like this:
DABO FM 2020