Labarai

Kungiyar Izala ta kai ziyarar jaje ga Sambo Dasuki kwanaki 3 bayan sakinshi akan zargin “Sata”

Kungiyar Izalatul Bidi’a wa Ikamatussunnah, karkashin jagorancin shugabanta, Sheikh Abdullahi Bala Lau, ta kai wa Kanar Sambo Dasuki ziyarar jaje zuwa gidanshi dake garin Abuja.

Hakan na zuwa ne kwanaki 3 bayan sakinshi da hukumar DSS tayi akan zarginshi da yin sama da fadi da kudaden da tsohuwar gwamnati ta ware domin siyan makaman yaki da ‘yan Boko Haram

DABO FM ta tattaro cewa shugaban kungiyar, Sheikh Bala Lau, ya bayyana Kanar Sambo Dasuki a matsayin mutum wanda ya taimakawa kungiyar wajen ayyukanta na yada addinin Musulunci, ya kuma ce Dasuki yana samun kamasho daga dukkanin ayyukan alheri da kungiyar take yi.

“Sai Allah ya bawa Sambo, kamasho. Saboda haka duk wannan ayyukanka ne, muna ta yada addinin Musulunci da yin wa’azi. Allah madaukakin Sarki ya baka lada ya kuma kara ma da hakuri. Allah Ya bada hakuri, Allah Ya bada hakuri.”

“Mun shigo gari, shiyasa muka ce sai munzo dukkanmu a kungiyance, mu nuna maka lallai abinda akayi mana, bazamu manta ba.”

Daga cikin wadanda suka samu rakiya, sun hada da Sheikh Muhammad Kabiru Gombe, Sheikh Yakubu Musa da sauran manyan jagororin kungiyar, kamar yacce Sheikh Bala Lau ya bayyana.

DABO FM ta binciko cewa a ranar 26 ga watan Nuwambar shekarar 2017, a wata hira da sashin Hausa na BBC, Sheikh Kabiru Gombe ya nesanta kungiyar Izala da zargin da ake yi mata na karbar kudaden makamai daga hannun Kanar Dasuki.

Sai dai ya tabbatar da cewa kungiyar ta karbi gudunmawa daga cikin wani shiri da gwamnatin shugaba Jonathan ta yi domin daukan matakai wajen magance matsalar ta’addanci a Najeriya.

Karin Labarai

Masu Alaka

A tantance jami’an tsaro domin ana zargin akwai hannun su a hare hare -Sheikh Sani Jingir

Muhammad Isma’il Makama

Kungiyar Izala tayi kiran Sanatoci da kada su tantance Ministocin da suke ‘yan Shi’a

Dabo Online

Neman Taimako: Kujerar gwamnan da ka hau ta gidanku ce? – Sheikh Jingir ga Masari

Dabo Online

Sheikh Bala Lau ya ziyarci filin masallacin da aka rusa a Fatakwal dake Jahar Ribas

Muhammad Isma’il Makama

Kudin Makamai: Abinda kayi mana, baza mu manta ba – IZALA ta fada wa Sambo Dasuki

Dabo Online

Daukar lauyan da ba Musulmi ba ya jawo wa IZALA cece-kuce

Dabo Online
UA-131299779-2