Hukumar dake kula da cututtuka ta Najeriya, NCDC ta sake tabbatar da samun karuwar masu dauke da cutar Covid-19 guda 20 a daren Juma’a.
Kamar yadda hukumar ta bayyana a shafinta na yanar gizo gizo da shafin Twitter, tace adadin wadanda aka tabbatar a Najeriya ya zama 210.
“A yau da misalin karfe 10:30 na dare an sake samun masu dauke da cutar ‘Corona Virus’ guda 20. An samu guda 11 a Lagos, 3 a Abuja, 3 a Edo, 2 a Osun da guda 1 a Ondo.”