//
Wednesday, April 1

Yanzu-Yanzu: Boko Haram na luguden wuta a Damaturu

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Yanzu haka dai a garin Damaturu dake jihar Yobe na fuskantar hare-hare wadda ake zargin Kungiyar Ahlul Sunnah Li Daawatu Wal Jihad wadda aka fi sani da Boko Haram.

Labari ya ishe Dabo FM a halin da ake ciki a garin na Damaturu tun kafin karfe 6 na yamman yau Lahadi ake jin fashewar wasu abubuwa da ake zargin bama bamai ne tare da harbe harbe.

Ya zuwa yanzu dai abin na ci gaba da faruwa kamar yadda mai bawa gwamnan jihar Yobe, Mai Malabuni shawara, Shariff Almuhajir ya bayyana.

Shaiff ya bayyana mana cewa “Yanzu haka muna tsakiyar fashe fashen wasu abubuwa masu kara, ga karar tashin bama bamai da harbi ba kakkautawa.”

Masu Alaƙa  Babu inda Boko Haram take da ko taku daya a Najeriya - APC

Tare da fadin suna bukatar addua domin suna cikin mawuyacin hali.

Da yake tabbatar da al’amarin, mai magana da yawun SOjojin Lafiya Dole, Njoka Irabor, ya bayyana cewa mayakan Boko Haram sunyi yunkurin shiga garin na Damaturu.

Sai dai ya tabbatar da tini Sojojin suka taka musu birki, ya ce zasu bayar da cikakken bayani akan hari a gobe.

Karin Labarai

Share.

Comments are closed.

%d bloggers like this:
DABO FM 2020