//
Saturday, April 4

Sojojin Saman Najeriya sun fatattaki mafakar Boko Haram a dajin Sambisa, sun hallaka da dama

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Rundunar Soji saman Najeriya karkashin dakarunta na Lafiya Dole, sun karkashe mayakan kungiyar Boko Haram a wani hari da rundunar da kai zuwa dajin Sambisa.

Kakakin rundunar, Ibukunle Daramola ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar a hedikwatar rundunar dake Abuja.

DABO FM ta tattaro cewar Ibukunle Daramola yace rundunar tayi sumamen ne a ranar Laraba da ta gabata.

Kamfanin dillancin labaran najeriya, ‘NAN’ ya bayyana cewar kakakin rundunar, Daramola, yace rundunar Sojin ta farwa mayakan Boko Haram dinne bayan da wani jirgin leken sirri na rundunar ya gano bindigar mayakan Boko Haram kirar BHT a kasan wata bishiya.

Ya kara da cewa sun gano tarin mayakan Boko Haram a karkashin bishiyar zagaye da bindigar kirar BHT.

Masu Alaƙa  Jami’an SARS sun kashe mayakan Boko Haram da dama a wata arangama da sukayi a Borno

Kakakin yace rundunar zata cigaba da zage dantse domin karar da ragowar mayakan Boko Haram da suka rage a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya.

Karin Labarai

Share.

About Author

•Sublime of Fagge's origin. •PR Specialist •PharmD candidate

Comments are closed.

%d bloggers like this:
DABO FM 2020