Home LabaraiYanzu-yanzu: Masarautar Zazzau ta karyata sanar da ganin watan Shawwal, tace akwai azumi gobe

Yanzu-yanzu: Masarautar Zazzau ta karyata sanar da ganin watan Shawwal, tace akwai azumi gobe

by Dabo Online
0 comments
Sarkin Zazzau

Masarautar Zazzau ta  jihar Kaduna, ta karyata rahotannin da aka yadawa cewa ta sanar da ganin sabon watan Shawwal.

DABO FM ta tattara cewar wani limami ne a  Zaria, ne ya fitar da sanarwar da sunan Sarkin Zazzau a kan shafinshi na Facebook.

AKan haka ne DABO FM tayi tattaki zuwa masarautar, mun kuma tattauna da jami’in hulda da jama’a na masarautar, Ciroman Shantalin Zazzau, Alhaji Abubakar Ladan, ya kuma nesanta Sarkin daga fitar da sanarwar.

“Wannan labarin bashi da tushe. Saboda haka, gobe 30 ga watan Ramadana kamar yadda Sarkin Musulmi ya sanar.”

 

You may also like

-
00:00
00:00
Update Required Flash plugin
-
00:00
00:00