Home LabaraiYanzu yanzu: Mayakan Boko Haram sun sace Sojoji 4 da ‘yan sanda 2

Yanzu yanzu: Mayakan Boko Haram sun sace Sojoji 4 da ‘yan sanda 2

by Dabo Online
0 comments

Rahotanni daga Jaridar The Cable sun bayyana cewa mayakan kungiyar ‘yan ta’addar Boko Haram sun sace jami’an Sojin Najeriya guda 4 da ‘yan sanda guda biyu.

Majiyoyin sun bayyanawa jaridar cewa mayakan sun dauke jami’an akan titin Damaturu zuwa Maiduguri.

Hakazalika sun bayyana cewa mayakan sun yi wa jami’an tsaron kwantan bauna a kusa da Kauyen Auno akan titin Damaturu zuwa Maiduguri.

“Mayakan da aka gani da kayan jami’an tsaro sun kashe hanya a kan titin da motoci kirar Hilux guda 3 kafin su dauke jami’an tsaron da suke dawowa daga hutun da suke tafi.”

“Jami’an tsaro 4 aka dauke a cikin wata mota mai kujeru 18, an dauke ‘yan sanda a cikin mota kirar Gulf.”

Cikakken bayani na zuwa…

You may also like

-
00:00
00:00
Update Required Flash plugin
-
00:00
00:00