Yau kwanaki 210 tin bayan zargin Kwamishinan Kano da warce takardar tattara sakamakon zabe

Karatun minti 1

A ranar Litinin, 11 ga watan Maris na shekarar 2019, jami’an ‘yan sanda jihar Kano sukayi awon gaba da tsohon kwamishinan kananan hukumomi na jihar Kano, Hon Murtala Sule Garo, zuwa ofishinsu.

Hakan na zuwa ne bayan zargin warce takardar tattara sakamakon zaben mazabar gama dake karamar hukumar Nassarawa a jihar Kano.

Lamarin da ya jawo sake gudanar da zabe a mazabar Gama da wasu wurare da hukumar INEC ta soke bisa rashin zaman lafiya.

Dabo FM ta bincika cewa daga ranar 11 ga watan Maris zuwa 6 ga watan Oktobar 2019, a kama kwanaki 210 dai-dai.

Sai dai tin bayan sake zaben da akayi, gwamnan jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje, ya lashe zaben gwamnan jihar duk da cewa dan takarar PDP, Abba Kabir Yusuf ne ke da rinjayen kuri’un a zaben farko.

Bayan ayyana Dr Ganduje, jami’iyyar PDP da dan takararta, Abba K Yusuf, suka garzaya kotu bisa kin amincewa da sakamakon zaben.

Ranar 2 ga watan Oktoba, kotun sauraren korafin zaben gwamnan Kano, ta jaddada gwamnan jihar Kano, Dr Abdullahi Ganduje, a matsayin halastaccen gwamnan jihar inda ta kuma kori karar.

Ta kuma bayyana cewa wakilin jami’iyyar PDP ne ya yayyaga takardar zaben mazabar Gama ba Kwamishina Murtala Garo ba.

Jami’iyyar PDP bata amince da hukuncin ba, ta kuma bayyana zata daukaka kara zuwa kotun Kaduna.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog