Labarai

Ina ganin laifin Talakawa, da mutum ya samu kudi sai su yanyameshi – Aisha Falke

Aisha Falke, yar kasuwa a Arewacin Najeriya ta dora Talakawa a matsayin masu alhaki wajen canzawar halin mutum da zarar sun samu kudi ko mulki.

DABO FM ta tattataro cewa; ta bayyana haka ne a shafin Northern Hibiscus yayin da take bada amsar tambayar “Meyasa mutane suke chanzawa da sun samu wani chanji ko sun samun kudi?”

“Tabbas kudi da mukami suna chanza mutane, “Ni nama fi ganin laifin Talakawa. Da mutum ya samu kudi ko mulki a bi a yanyameshi kamar shazumami ya ga Sikari.”

“Abinda yafi dauremin kai shine yacce matan masu kudi ko mulki suka daura wa kansu wani abu (Nuna isa da dagawa)”

Hajiya, Kudi da mukamin duk ba mai dorewa bane, kuma ba naki bane, na Mijinki ne, ba kece ki kayi wahalar ba, kawai dai sa’ar aure kika yi.”

Daga cikin masu mata martani a shafin, Dabo FM ta gano wata mai suna Fa’iza Amin, inda tayi nuni da cewa suma mawallafan shafukan sada zumunta suna bada tasu gudunmawar wajen chanzawar halayen masu kudi.

Inda tace kullin abubuwan da suke wallafawa, wadanda suka shafi masu kudi ne kadai.

“Ban taba ganin kun wallafa bikin Talaka ko wani abu da yayi na birgewa ba, kullin sai kuranta masu kudi, don haka dole kuwa suyita daga kai.”

Masu Alaka

Naman Sallah hakkin Iyayen Samari ne – Martanin ‘Yan mata zuwa ga Samari

Dabo Online

‘Yan Matan Arewa sun bukaci a fara yiwa mazaje gwajin hauka kafin a daure musu aure

Dabo Online

Zauren Maza da Matan Arewa a Instagram ya hada dubu dari 850 don tallafawa Jarumi Moda

Dabo Online

Jarumar barkwanci ‘yar kudancin Najeriya ta yi batanci akan Musulunci

Dabo Online

An daura wa yaro dan shekara 15 aure da budurwarshi ‘yar 14 bayan yayi mata ciki

Dabo Online

‘Yan Mata sun fara kokawa kan yadda samari sukayi ƙememe suka hana su kayan Sallah

Dabo Online
UA-131299779-2