//
Thursday, April 2

Yau watan Yuli yake 35 a jihar Kano – Ma’aikata a jihar sun koka bisa rashin Albashi

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Ma’aikatan gwamnati a jihar Kano sun koka kan yacce gwamnatin jihar tayi ke-me-me da batun biyansu albashi na watan Yuli.

Duba da karatowar Sallah babba, ma’aikatan sunyi kira da babbar muryan don gwamnati ta sauke nauyin hakkin da ya rataya a wuyanta.

DABO FM ta samu sakonni daga ma’aikatan gwamnatin musamman Malaman makaranta, inda suka bayyana mana cewa sun tsinci kansu a cikin wani mawuyacin hali dalilin rashin biyan albashin da gwamnatin bada yi ba.

“Yau wata 35” inji ma’aikatan. Ma’ana har watan Agusta ya shiga da kwanaki biyar amma gwamnatin bata biyasu kudinsu.

DABO FM ta gudanar da nata binciken dan tabbatar da lamarin. Yayin tattaunawarmu da wasu malaman makaranta sun bayyana mana cewa “Muma har yanzu bamu ji alaat.”

Masu Alaƙa  Gwamnatin Kano ta dauki kwararru don koyawa Matasan jihar Sana’o’i

Ko ya dace gwamnati ta ki biyan ma’aikatanta albashi a kan kari musamman a irin wannan lokaci na hidundumun Sallah?

Bayyana ra’ayi a kasan wannan rubutun.

Karin Labarai

Share.

About Author

Comments are closed.

%d bloggers like this:
DABO FM 2020