Me ya faru da Adam A Zango yake ta barin na zance na babu dalili a Instagram?

Tin a makon da ya gabata ne fitaccen jarumin a masana’antar Kannywood, Adamu Zango yake ta hakilon zance.

DABO FM ta bibiyi Adam Zango bisa irin kalaman da yake ta furtawa wadanda suke kama da habaici, nuna dagawa dama shawarwari.

Mafi akasarin lokuta, duk masu bibiyar Jaruman Kannywood zasu gane cewa Adam Zango, mutum ne mai surutun dadi da na babu dadi.

A dai cikin makon, a ranar Talata, Adam Zango ya kara furucin cewa shine wanda daya fi kowanne jarumi a masana’antar fice a duniya, sai dai wannan karon ya bayyana cewa a mawakan Gambara na Hausa Hip-Hop.

A wani hoto daya wallafa kuma, Zango yayi furucin cewa “Kubar Karnuka suyi ta haushi” a yayin da ya wallafa hotonshi tsakanin matashin mawaki dan jihar Legas, Adeem Lyta mai sabuwar wakar Monalisa da ta zama gwarzon mako.

Ko me kuke ganin yake tunzura Zango yayi ta surutai?

Bayyana ra’ayinku a kasan wannan rubutun.

%d bloggers like this: