Home LabaraiIndiya: Magidanta 1,774 ne suka kai karar matansu yayin dokar zaman gida a watan Afrilu

Indiya: Magidanta 1,774 ne suka kai karar matansu yayin dokar zaman gida a watan Afrilu

by Dangalan Muhammad Aliyu
0 comments

Magidanta 1,774 ne suka debo wa matansu ‘yan sanda yayin dokar zaman gida a kasar Indiya.

Yayin kududduga da wata kungiyar kare hakkin maza ma’aurata ta SIF tayi, tace a iya watan Afrilu aka samu adadin mazan da suka kai koken matansu ga kungiyar.

DABO FM ta tattara cewar tin a ranar 13 ga watan Maris, gwamnatin kasar Indiya ta sanya dokar hana fita gaba daya kasa.

Haka zalika a yau, 1 ga watan Mayu, gwamnatin kasar ta kara tsawaita dokar har zuwa 17 ga wata.

Kungiyar tace mazan sun fuskanci tsananin cin zarafin tin bayan da aka sanya dokar zaman gida a kasar ta Indiya, kamar yadda Jaridar Indian Express ta kasar ta rawaito.

Sai dai tace kiran da mazajen da ake ci wa zarafi ya ragu da kashi 40 tin bayan da aka sanya dokar hana fita, duk da a cewar kashi 90 na mazan da ake ci wa zarafin ba sa iya kai korafinsu saboda barazanar da matan ke yi musu.

Ta kuma kara da cewar wayar da ta samu ta karshe a watan Afrilu, wani miji ne dan shekara 30 da matarshi mai shekaru 28 ta ci zarafin a dalilin ya hana ta tafiya garin iyayenta da suke da zama a garin Lucknow na jihar Uttar Pradesh.

Shugaban kungiyar, Maninda Singh yace mazaje a daga jihohin Uttar Pradesh, Bihar, Jharkhand, da Uttarakhand ne suka fi kawo korafi da adadin 356, da misalin 10 na dare.

Maza 58 daga jihar Karnataka, 88 daga Punjab da Himachal Pradesh, 9 daga Tamil Nadu.

313 daga jihohin Rajasthan, Hariyana, Jammu & Kashmir da birnin Delhi. 24 daga jihar Andhra Pradesh da Telengana, 46 daga West Bengal da sauraran sassan Arewa maso gabashin kasar.

185 daga Gujarat da Maharashtra, 110 daga MP da Chhattisgarh da guda 9 daga cikin Kerala.

You may also like

-
00:00
00:00
Update Required Flash plugin
-
00:00
00:00