Za’a gudanar da Zaben kananan hukumomi ranar 27 a jihar Zamafara

Hukumar zaben jihar Zamafara ta ZIEC ta fitar da ranar 27 ga watan Afrilun 2019.

Baturen zaben jihar ta Zamafara, Garba Muhammad ne ya bayyana haka ne yau Litinin a taron da yayi da manema labarai.

Daily Trust tace, Wa’adin shuwagabanni kananan hukumomin jihar ya kare tin ranar 2 ga watan Janairun 2018, sai dai majalissar jihar ta kara wa’adin zuwa watan Mayu.

Jihar Zamafara dai tana cikin wani matsananci hali na kashe-kashe da sace sacen mutane.

Al-kaluman mutanen da suka rasa rayukansu ya kai sama da mutane 3000.

Inda wasu ‘yan bindiga sukan afkawa gari tare da yin harbin kan mai uwa da wabi, sace mutane domin yin garkuwa, wani lokacin har sukan bi shanu su yanka ko su tafi dasu.

Karin Labarai

Comments are closed, but trackbacks and pingbacks are open.