Takaitattun Labaran Yammacin Yau

Karatun minti 1

Kotun daukaka kara ta mayar wa da Ibrahim Baba na APC kujerar sa a Filato.

Duk da matsalar tsaro, za a gudanar da zabukan kananan hukumomi a ranar 27 ga watan Afrilu a jahar Zamfara.

Ministan tsaro, Mansur Dan-Ali ya ce furucinsa baya nufin kaskanta sarakunan gargajiya. ‘Yan bindiga sun salwantar da rayukan Mutane 15, sun raunata mutane 14 a jihar Nasarawa.

Kotun hukunta ma’aikatan gwamnati CCT ta ayyana ranar Alhamis 18 ga watan Afrilu, 2019 matsayin ranar da za a yanke hukunci kan tsohon Alkalin alkalai, Walter Onnoghen.

Kasafin Kudi: ASUU ba ta lamunci tanadin da gwamnati ta yi wa ilimi ba.

Hukumar kiyaye hadura ta kasa, FRSC ta bukaci gwamnati ta ba su makamai domin kare kansu.

Gwamnatin Zamfara ta jinjina ma gwamnatin tarayya kan haramta ayyukan hakar ma’adinai a jihar.

Akwai bukatar Buhari ya maida hankali akan kashe-kashen da ke faruwa a Arewa, inji Dattawan Arewa.

Ministan kudi ta ce babu tunanin janye tallafin mai a yanzu.

Buhari ya nemi goyon bayan kasashen dake makwabtaka da Najeriya wajen kare yaduwar makamai.

Dakarun sojin Isra’ila sun kama Falasdinawa 10 a Yammacin Gabar Kogin Jordan.

Yara kanana 7 ne suka rasa rayukansu sakamakon wani bam da aka tayar a jihar Lagman da ke Afganistan.

Karin Labarai

Dangalan Muhammad Aliyu

•Sublime of Fagge's origin.
•PharmD candidate

Latest from Blog