Kiwon Lafiya Labarai

Za’a yi wa yaron da aka haifa babu ‘Dubura’ tiyata kyauta

Za’a yi wa Sa’idu, mai shekaru 4 kacal a duniya dan asalin garin Pataskum ta jihar Yobe, tiyata biyo bayan rashin haifarshi da akayi da dubura.

DABO FM ta tattaro cewa za’ayi wa Sa’idu aikin ne kyauta a cikin watan Janairun 2020 a asibitin koyarwa na Mallam Aminu Kano dake jihar Kano.

Hakan na zuwa ne bayan daukar nauyin aikin da wani bawan Allah yayi ta sanadin karanta labarin yaron a jaridar Daily Trust, makonni biyu da suka gabata.

Da yake shaidawa jaridar Daily Trust, mahaifin Sa’idu, Mallam Muhammad Babi, ya bayyana yacce wanda ya dauki nauyin aikin ‘danshi ya kirashi ta wayar tarho tare da shaida masa zai dauki nauyin aikin yaron kyauta.

Ya kara da cewa, ya hada shi da wani ma’aikacin asibitin koyarwa na Mallam Aminu Kano domin fara binciken abinda ya dace ayi wa Sa’idu. Yace duk da cewa anyi dasu zasuje Kano a ranar Litinin, tin ranar Asabar ya isa Kano don kaucewa saba lokaci.

“Cikin gaggawa bayan kiran mutumin, na sanar da abokan aiki na na tashar mota, suka hada min abubuwan da zan bukata na tafiya da kuma cin abinci.”

Ya kara da cewa bayan sun isa asibitin, Likitoci sun bukaci sunyi gwaje-gwaje kafin aikin wanda zuwa yanzu an kammala.

Ya shaida an saka ranar 13 ga watan Janairun 2020 a matsayin ranar da za’ayiwa Sa’idu tiyata.

Ya bayyana godiyarshi ga duk wanda suka taimaka masa tin bayan lokacin da Daily Trust ta wallafa labarin Sa’idu.

Haka zalika ya godewa kamfanin Media Trust da suka buga labarin.

Masu Alaka

Yadda za mu kare kan mu daga kamuwa da cutar zazzabin ‘Lassa’ -Dr Abdul’aziz T. Bako

Muhammad Isma’il Makama
UA-131299779-2