Siyasa

Atiku, Kwankwaso, Tambuwal, Saraki, Lamido? PDP ta tsunduma neman dan takarar 2023

Shugaban kwamitin amintattu na jam’iyyar PDP, Sanata Walid Jibrin, ya bayyana cewa jam’iyyar ta shiga neman nagartaccen dan takara wanda zai tsaya mata a zaben shugaban kasa a zaben 2023.

Dabo FM ta tattaro cewa; Walid ya furta hakan ne a garin Kaduna inda ya kara da cewa kowa na da damar tsayawa takara muddin ya cika ka’idojin jam’iyyar.

Da aka tambaye shi shin ya batun tsohon dan takarar da jam’iyyar ta tsayar a zaben 2019, sai ya kada baki yace, “Atiku na da damar tsayawa kamar kowane dan takara idan yana da sha’awa.”

“Kana tinanin Atiku ne kadai mai bukatar tsayawa takara? Bana tinanin akwai matsala don wani ya nemi takara a kowanne bangare yake a Najeriya.”

“Amma shawarwarin da muka harhada sune zasu dora mu akan hukuncin dam takarar da zamu fitar.” Kamar yadda jaridar Punch ya bayyana.

Cikin satin nan da muke ciki dai bayan fitowar tsohon mai bawa shugaban kasa shawara a fannin tsaro, Sambo Dasuki wasu suka fara fitar da hotuna na neman tsayawar sa takarar shugabancin kasa.

Karin Labarai

Masu Alaka

Kwankwaso ya nuna takaici da bakin ciki akan kashe-kashe da sace-sacen Mutanen Arewa

Dabo Online

Na’urar tattara zabe ta INEC ta nuna Atiku ne ya lashe zaben 2019 – PDP

Dabo Online

Nima na cancanci samun kyautar wanzar da zaman lafiya ta ‘Nobel Prize’ -Buhari

Muhammad Isma’il Makama

Adamawa: Ganduje, El- Rufa’i na shirin kawo ‘Yan Sara-Suka domin tafka magudi – PDP

Dabo Online

Kwankwaso ya tura matasa neman Ilimi, Ganduje ya bude cibiyar koyar da gyaran mota

Dabo Online

Ina tsoron karawa da Kwankwaso – Shekarau

Dabo Online
UA-131299779-2