Home Labarai2023: PDP ta shiga neman sabon dan takarar shugabancin kasa da zata tisa a gaba

2023: PDP ta shiga neman sabon dan takarar shugabancin kasa da zata tisa a gaba

by Muhammad Isma’il Makama
0 comments

Shugaban kwamitin amintattu na jam’iyyar PDP, Sanata Walid Jibrin ya bayyana cewa jam’iyyar ta shiga neman nagartaccen dan takara wanda zai tsaya mata a zaben shugaban kasa a zaben 2023.

Rahoton mu na nan Dabo FM ya bayyana cewa Walid ya furta hakan ne a garin kaduna inda ya kara da cewa kowa na da damar tsayawa takara muddin ya cika ka’idojin jam’iyyar.

Da aka tambaye shi shin ya batun tsohon dan takarar da jam’iyyar ta tsayar a zaben 2019, sai ya kada baki yace, “Atiku na da damar tsayawa kamar kowane dan takara idan yana da sha’awa.”

“Kana tinanin Atiku ne kadai mai bukatar tsayawa takara? Bana tinanin akwai matsala don wani ya nemi takara a kowanne bangare yake a Najeriya.”

“Amma shawarwarin da muka harhada sune zasu dora mu akan hukuncin dam takarar da zamu fitar.” Kamar yadda jaridar Punch ya bayyana.

Cikin satinna dai bayan fitowar tsohon mai bawa shugaban kasa shawara a fannin tsaro, Sambo Dasuki wasu suka fara fitar da hotuna na neman tsayawar sa takarar shugabancin kasa.

You may also like

-
00:00
00:00
Update Required Flash plugin
-
00:00
00:00