Zaben Gwamna: Wasu bata gari sun cinnawa ofishin INEC wuta a jihar Benue

Karatun minti 1

Wasu bata gari da ba’a san ko suwaye su ba, sun cinnawa ofishin hukumar zabe ta INEC wuta dake jihar Benue.

Matasan sun sakawa ofishin wuta ne kafin a raba kayyakin zabe zuwa mazabu inda ake saka ran kada kuri’a a safiyar yau da za’a gudanar da zaben gwamnoni tare da ‘yan majalissun jiha a fadin tarayyar Najeriya.

Da take magana,  Mrs. Ngunan Yogo, shugabar hukumar reshen jihar ya bayyanawa manema labarai cewa bata garin su kone duk wani kayan aiki da aka tanada saboda gudanar da zabe.

Wani mai shedar gani da ido yace, bata garin sun fara sakin harbi ne a kofar hukumar kafin su kai ga sakawa ofishin wutar da tayi sanadiyyar konewar ofsihin kurmus.

“Babu asarar rai ko kuma rauni, saidai duka kayayyakionmu sun kore kurmus a lokacin da muke shirin raba su zuwa mazabun cikin jihar Benue.” – Mrs. Ngunan Yogo

Karin Labarai

Dangalan Muhammad Aliyu

•Sublime of Fagge's origin.
•PharmD candidate

Sabbi daga Blog