Zagin Dr Ahmad Gumi don ya sabawa ra’ayinka, Daga Salisu Webmaster

dakikun karantawa

ZAGIN DR AHMAD GUMI DON YASA BAWA RA’AYIN KA

Duk lokacin da kake ganin Malam ya fadi wani abu da ya sabawa ra’ayinka sannan ka shigo wannan fage ka zage shi ko ka ci masa mutunci to ka sani aikin banza kake yi saboda wadannan dalilai.

Kai da ka sabawa malam waya zage ka?

Shi malam ya taba shiga shafin wani da ya sabawa ra’ayinsa ya zaga?

[irp posts=”4104″ name=”Kada Atiku ya yarda da sakamakon zabe, domin magudi akayi – Dr Ahmad Gumi”]

Shin lokacin da malam yaje yayi karatu akwai taimakonka ko na iyayenka ballantana kace kada yayi maganar da ta saba maka?

Shin lokacin da malam ya dawo wannan kasa domin ya fara gabatar da karatu akwai gudunmuwarka, da har zaka ce kada ya saba maka?

Shin dole ne sai ra’ayinka da malam yayi daidai a duk abin da zai fada?

Shin dole sai malam yaji tsoronka da tunanin idan ya saba maka zaka dakile abincin da kake bashi?

Shin ka taba jin wani dan siyasa ko shugaban wata kungiya ya fada cewar ya taba taimakawa malam da wani abu?

Shin idan ra’ayinka yayi daidai da na malam, malam ya taba aiko maka da godiya ko kudi.

Shin dole duk abin da malam zai fada sai yayi daidai da ra’ayin da gwamnati ke so?

Lokacin da Malam ya hango matsala a turken wutar lantarki ta Kainji kuma ya sanar da shugaban kasa a wancan lokacin kai ka sani?

Ko kuma dawowarshi a 2003 ya roki wanda kake zagin malam saboda da shi a yanzu da ya tsaya takarar shugaban kasa har ya amince, to, da kai aka yi?

Ku sani duk zagin da zaku yi domin Malam ya sabawa ra’ayinku ba zai cutar da shi da komai ba, hasalima HAUSHIN KARE BA ZAI HANA GIRGIJE A SAMA TAFIYA BA.

Ku lura da kyau, ku kuma natsu, ku kuma saurari abinda malam yake kira da ayi, MASLAHAR AL’UMMA NE DA YADDA ZA A CI NASARA A RAYUWA.

Babu abin da malam ya ke hange da kuma aikatawa sai abin da Allah Yake so kuma ya yarda da shi.

Idan har abinda Malam yake fada bai sabawa Allah da Manzonsa ba, kai aka sabawa to kaje AN SABA MAKA!!

 

Karin Labarai

Dangalan Muhammad Aliyu

•Sublime of Fagge's origin.
•PharmD candidate

Sabbi daga Blog