0
A yau Juma’a, 15/03/2019, aka sace babban malamin addinin musulunci kuma mahaddacin al’qurani, Sheikh Ahmad Muhammad Sulaiman Kano.
An dai sace malamin ne tare da ‘yayanshi guda 6, a kan hanyar dawowarsu daga Birnin Kebbi.
Tini dai addu’o’i da sallali na cigaba da gudana a fadin kasashen arewa domin Allah ya bayyana malamin.
Har zuwa kawo yanzu ba’a ji daga bakin malamin ko wadanda suka sace shi ba.
Muna addu’a Allah ya bayyana shi.
