Home Labarai“Sai randa kuka kawo takardar biyan kudin wuta zamu tsunduma namu yajin aikin”

“Sai randa kuka kawo takardar biyan kudin wuta zamu tsunduma namu yajin aikin”

by Muhammad Isma’il Makama
0 comments

Yan Najeriya sun maida wa ma’aikatar lantarki ta National Union of Electrical Employees (NUEE) martani game da barazanar yajin aikin da suke kokarin sake tsundumawa.

Rahoton da Dabo FM ta hada ya nuna daruruwan yan Najeriya sun nuna fusatar su ga shirin yajin aikin da ma’aikatan lantarki ke kokarin komawa.

Inda mutane da yawa sukayi barazanar kin biyan kudin wutar da suka ce ai bama kawota ake ba.

“Zuwa ga Nepa ko PHCN kodai ma me ake kiran ku, ina so kusan ni sai ran da kuka kawo bill karshen wata zan tafi nawa yajin aikin, Nagode.” Inji wani mai suna @CruscioComedy a shafin Twitter.

@FUnyeoziri shima yace “Dama kun sani baku sanar da yajin aikin ba, da zai zama kamar kowacce rana tunda ba wutar muke samu ba.”

Haka dai akayi ta martani iri-iri, daga karshe dai zuwa yanzu bamuji janyewa ko sulhu tsakanin masu ruwa da tsaki na kamfanin da sauran ma’aikatan nasu ba.

You may also like

-
00:00
00:00
Update Required Flash plugin
-
00:00
00:00