Labarai

Duk da shirin sasanta tsakani, Sarki Sunusi ya kori ‘Sokon Kano’ daga fada

Mai marataba Sarkin Kano, Mallam Muhammadu Sunusi II, ya kori Sokon Kano, Alhaji Ahmad Abdulwahab daga fadar Masarautar Kano.

Hakan na zuwa ne cikin kasa da awanni 24 da kwamitin da tsohon shugaban Najeriya, Abdulssalam Abubukar, ya roki Sarki Muhammadu Sunusi da gwamna Ganduje dasu dakatar da duk wani shirinsu na cigaba da rigimar har zuwa sanda kwamitin zai sasanta tsakanin nasu.

DABO FM ta tattaro cewa an alakanta korar Sokon Kano daga fada ne bisa wasu kalaman rainuwa da nuna kaskanci da yayi akan Sarki Sunusi a ranar taron yaye dalibai a makarantar horar da ‘yan sanda dake garin Wudil.

Sokon Kano, daya daga cikin fadawan Sarkin, ya fito a wani faifan bidiyo dake ta yawo a kafafen sadarwa wanda aka ganshi yana fadar magan-ganu akan Sarkin Kano. – Kamar yacce Daily Trust ta rawaito.

Da yake tabbatar da lamarin, Sokon Kano, ya shaidawa Daily Trust yacce ta kasance.

“Yau da safe (A jiya Litinin), naje fada. Na shiga cikin sauran masu hidimtawa Sarki, mun rakashi, bayan Sarki ya zauna a wajen da yake zama. Shugaban ma’aiakta fadar ya tunkaro ni.”

“Ya tuhumeni cewa me ya kawo ni cikin fada, na ce masa nazo ne nayi aiki na kamar yacce nasab. Yace min ba’a bukata ta a cikin fadar, bazan yi alaka da makiyan fadar ba kuma in dawo cikin fada.”

“Daga nan ya umarceni da in fita daga cikin fadar.”

Ya kuma kara da shugaban ma’aikatan cikin fadar ya aike da jami’an ‘yan sanda da suke aiki a fadar da suyi waje dashi.

Sai dai haka ya gaza cimma ruwa wajen jin ta bakin masarautar akan batun.

Masu Alaka

Ganduje ya bijirewa umarnin Kotu, ya nada sarakuna 4 daya ƙirƙira

Dabo Online

Tsugunno: Masu nadin Sarki a masarautar Kano sun maka Ganduje a kotu

Dabo Online

Sarkin Kano, Sunusi II ya mayarwa da Ganduje martani a karon farko

Dabo Online

Wata babbar Kotu ta dakatar da umarnin kama akantan Sarkin Kano Muhammadu Sunusi II

Dabo Online

Rikicin Masarautu: Masu nada Sarki sun kara maka Ganduje a kotu

Muhammad Isma’il Makama

Manyan bukatu 5 da Ganduje yake so majalisa ta zartar masa kan masarautar Kano

Muhammad Isma’il Makama
UA-131299779-2