Tue. Nov 19th, 2019

Dabo FM Online

World’s First pure Hausa online Radio

Zan fi bawa Talakawa kulawa a wannan zangon – Buhari

2 min read

Shugaba Muhammad Buhari yace zai kula da sha’anin Talakawa a zangon mulkinshi na 2.

Shugaba Buhari ya bayyana haka ne a ranar Talata lokacin da yake wata ziyarar barka da Sallah da Hakiman masarautar Daura suka kai masa a gidanshi dake garin Daura na jihar Katsina.

Shugaban ya kara da cewa; zuwa yanzu ‘yan Najeriya sun san waye shi tare da manufofinshi, wanda a cewarshi yace shine dalilin daya saka aka kara zabarshi a karo na biyu da kuri’u masu yawa.

“Kun san dai yacce na bautu kafin zuwana wannan matsayin.

Nayi takara sau 3 a baya. A na hudun, cikin ikon Allah, ya kawo na zama. A karawa ta ta 5, na zagaye jihohin kasar nan baki daya. Mutane sun fito kwansu da kwarkwata.

“Kuri’un da na samu ya nuna cewa mutane sun gane ni tare da manufofina. Gwamnatin mu zata aiwatar da alkawuran data dauka lokacin zabe na samar da Tsaro, bunkasa tattalin arziki da yaki da cin hanci da rashawa. Zamu tabbatar da nasarar marasa karfi.”

DABO FM ta bincika cewa shugaba Buhari yayi nuni da cewa ya baiwa bangaren noma da kiwo yanada matukan muhimmanci a gwamnatinshi, inda ya alkauranta nada gogaggen kuma kwararren Ministan Gona da albarkatu.

“Wanda yake da Ilimi tare da sanin yacce za’a kara samun riba da masu zuba jari.”

“Zan nada Minista wanda yasan bannin Gona tare da bangarorinshi na samar da ayyukan yi da habbaka tattalin arziki.

Kun ga dai yacce muka karya farashin taki a kasar nan, zamu cigaba da yin abubuwan dadadawa manomanmu. Noma shine karfi da madogararmu.”

©2019 Dabo FM Online. Sponsored by Dabo Media Group | Newsphere by AF themes.