Hukumar kare hakkin Musulman duniya ce zata dauki nauyin jinyar Al-Zakzaky ba ‘yan Shi’a ba

Rahotanni da dama sun fito akan cewa wata kungiyar ‘yan Shia ta kasar Indiya ce zata dauki nauyin jinyar da Sheikh Zakzaky yakeyi a kasar Indiya.

Inda wasu rahotannin ma suka bayyana wani hamshakin dan kasuwa a birnin New Delhi a matsayin wanda ya alkauranta daukar nauyin jinyar.

Sai dai binciken DABO FM daga wakilanmu da suke kasar ta Indiya, sun tabbatar da rashin gaskiyar rahotannin.

Suma na nasu bangaren, Ofishin Al-Zakzaky ta hannun shafinsh na Twitter sun karyata batun.

Sun bayyana cewa hukumar kare hakkin Musulmai ta duniya wacce take da zama a kasar Birtaniya ce zata dauki nauyin jinyar shugaban kuma jagoran Shi’a a Najeriya.

DABO FM ta binciko daga Jaridar Ahlul Bayt ‘ABNA’, babbar jarida yake kawo rahotanni akan mazahabar Shi’a, ta karyata batun daukar nauyin jinyar Sheikh Zakzaky da akace ‘yan Shi’a zasuyi.

Binceken na Dabo FM ya kara bincika shafukan sadarwa na manyan kungiyoyin Shi’a a kasar Indiya domin samun karin bayanai.

Sun bayyana cewa: “Hukumar kare hakkin musulman Duniya ta kasar Birtaniya ce zataa dauki nauyin jinyar Al-Zakzaky.

Wannan kungiyar ce ta dauki nauyin Sheikh Sahab a ‘yan watannin da suka wuce.

“Don haka karku yarda da labarai da suke cewa wani hamshakin dan kasuwa ko wata kungiyar Shia ce zata dauki nauyin Al-Zakzaky.” – Daga Shafin Hindi Resistance 2

Zuwa yanzu DABO FM ta tura da sakon jin karin bayani zuwa ga kungiyar IHRC domin jin karin bayani.

Karin Labarai

Comments are closed, but trackbacks and pingbacks are open.