Sun. Oct 20th, 2019

Dabo FM Online

World’s First pure Hausa online Radio

Sashin Jami’ar ABU Zaria ya baiwa Anas Umar mai hoton Sarkin Kano Sunusi II lambar yabo

1 min read

Sashin shugabancin daliban Jami’ar Ahmadu Bello Zaria ta karrama mai hoton Sarki Kano Muhammadu Sunusi II da lambar yabo a wani taro da ta shirya a makon daya wuce.

Anas Umar wanda aka fi sani da AU Tumbin Giwa, ya yi suna wajen daukar hotunan Masarautar Kano. Duk da cewa yana gudanar da kamfanin yin hotunan biki da tarurruka, AU Tumbin Giwa yafi yin shura wajen yiwa mai martaba Sarkin Kano hotuna.

Sashin shugabancin daliban ya bayyana cewa; sun bashi lambar yabon ne bisa irin kyawawan hotunan da yake dauka wadanda suka kara fito da girma da darajar Masarautar Gargajiya a idon duniya.

ABUSRC ta yi masa lakabi da ‘Allon samfuri na masu daukar hotunan Masarauta.’

Taron mai taken “Hall of Fame” ya samu halartar mutane daban-daban inda aka tattauna akan matasa da ayyukan yi da dai sauran maudu’ai.

Ga wasu daga cikin hotunan Anas Umar;

©2019 Dabo FM Online. Sponsored by Dabo Media Group | Newsphere by AF themes.