/

An yi kira ga Sarkin Zazzau da yin amfani da damarsa wajen sama wa matasa ayyukan yi

dakikun karantawa
Dr Nuhu Ramalan tare da Mai Martaba Sarkin Zazzau
Dr Nuhu Ramalan tare da Mai Martaba Sarkin Zazzau

An shawarci mai Martaba Sarkin Zazzau Ambasada Malam Ahmad Nuhu Bamalli, ya yi amfani da damar da ya samu wajen samar da aikin yi ga matasa, don kauce wa zaman kashe wando.

Dr. Nuhu Ramalan Jibril na sashin koyar da kimiyyar siyasa na makarantar horas da malamai ta kasa dake Zaria FCE, Ya fadi haka a lokacin da zuri’ar Malam Ramalan Jibril, suka kaiwa Sarkin ziyara a fadar sa.

Ya ce, sun kawo ziyaran ne saboda alaka biyu da ke tsakanin su da mai martaban, inda ya ce mahaifin sa Malam Ramalan aminin Marigayi Magajin Garin Zazzau ne, wato mahaifin Sarkin na Zazzau, kuma kakan sa Salahatu Azumi, jikan Sarkin Zazzau Abubakar ne Dan Sarkin Zazzau Musa.

Shi yasa suka kai ziyarar ban girma tare da mubaya’a ga sabon Sarkin da kuma yin addu’an fatan alheri.

Dakta Nuhu Ramalan, ya baiwa Sarkin littafai da ya wallafa a fannin Siyasar Duniya, inda ya jadda kira kiran ga Sarkin don ganin an kalli matsalan rashin aikin yi ga matasa.

Da yake mai da jawabin, Mai Martaba Sarkin Zazzau Ambasada Ahmad Nuhu Bamalli, ya gode wa zuri’ar gidan Malam Ramalan Jibril, na kawo masa ziyara ban girma, ya ce zai yi bakin kokarin sa don ganin matasa sun dogara da kan su.

Inda ya ce, wannan alaka a tsakanun su zai cigaba, kuma ya yi addu”ar samun zaman lafiya a masarautan Zazzau da Jihar Kaduna da kuma kasa baki daya.

Ziyarar dai ya sami halartar daukacin zuri’ar Malam Ramalan Jibril karkashin jagorancin Dakta Nuhu Ramalan na sashin koyar da kimiyyar Siyasa na makarantar horas da malamai da ke Zaria FCE.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog