Kiwon Lafiya Labarai

Zazzabin ‘Lassa’ yayi sanadiyyar mutuwar manyan Likitoci 2 a Kano

Wasu manyan Likitoci dake aiki a asibitin koyarwa na Mallam Aminu Kano a Kano, sun gamu da ajalinsu sakamakon kula da wata baiwar Allah da ake zargin tana dauke da zazzabin nan na ‘Lassa’.

Sanarwa daga asibitin ta bayyana rasuwar Dr Habibu Musa Fagge wanda ya rasu a ranar Litinin ta jiya da Dr Ummu Kultham wacce ta rasu ranar Juma’a.

A nata bangaren, kungiyar Likitocin Najeriya reshen jihar Kano ta fitar da matakin binciken kafatanin ma’aikatanta da suka kusanci mara mara lafiya.

A sanarwar da kungiyar ta fitar wacce ta DABO FM ta ganewa idanu, ta bayyana cewa tini dai kungiyar tace ta aike da wadanda ake zargin cutar ka iya shafa zuwa cibiyar kebantar da wadanda ake tunanin suna dauke da babbar cuta dake ‘Yargaya.

“Za’a kebantar da dukkanin wadanda suka kusanci mara lafiyar.”

Haka zalika, kungiyar ta bayyana cigaba da binciko wadanda suka lura da matar, ta kuma kira da wadanda suka san kansu su kai kansu domin agajin gaggawa.

Da Kano Focus ta tuntubi hukumar Asibitin na Mallam Aminu Kano, sun bayyana cewa suna cikin wata ganwar sirri, sai dai sun tabbatar yin taron manema labarai idan sun kammala.

Masu Alaka

Agwaluma na rage karfin maza -Binciken Masana daga Jami’ar Madonna

Muhammad Isma’il Makama

Likita ya ciro Kifi mai rai a hancin Yaro

Dabo Online

Diclofenac yana kara janyo afkuwar ‘Bugawar Zuciya’ da kaso 50

Dangalan Muhammad Aliyu

Zogale yafi kaza: Najeriya zata shuka zogalen naira Biliyan 9

Muhammad Isma’il Makama

Barin kumfar man goge baki a baka na inganta lafiyar hakora -Binciken Likitoci

Muhammad Isma’il Makama

Cin Nama yana kara yawaitar wari a jikin ‘Dan Adam – Masana

Dabo Online
UA-131299779-2