(function(w,d,s,l,i){w[l]=w[l]||[];w[l].push({'gtm.start': new Date().getTime(),event:'gtm.js'});var f=d.getElementsByTagName(s)[0], j=d.createElement(s),dl=l!='dataLayer'?'&l='+l:'';j.async=true;j.src= 'https://www.googletagmanager.com/gtm.js?id='+i+dl;f.parentNode.insertBefore(j,f); })(window,document,'script','dataLayer','GTM-P27NM8L');

Gidauniyar tallafa wa marayu da iyaye mata ta karrama wasu masu taimaka wa gidauniyar a Kaduna

dakikun karantawa

Duba da da irin gudummuwar da wasu daga cikin al’umma ke baiwa marayu, ya sa gidauniyar tallafawa marayu da iyayen su mata a karamar hukumar Zaria Jihar Kaduna karrama wasu mutane da lambobin yabo da suke bada gudummuwar su don cigaban marayu a Jihar Kaduna.

Daga cikin wadanda aka karrama sun hada da Barrista Abdullahi Lawal Muh’d da Mista Ikoko da Halima Aliyu kofar Doka na Ditv/Alheri redio Zaria da Misis Exter da kuma Yusuf Jibril na gidan redion Jihar Kaduna ksmc da sauran su.

Da take jawabin maraba a wurin taro, Uwar kungiyar marayun malama Adama Muhammad, ta ce irin gudummuwar da wadan da aka karrama suka bayar abin a yaba ne, a bangaren ilimi da tarbiyar marayu da daukan nauyin karatun su da kuma yin masu sutura.

Shi ma da yake nasa jawabin, Hakimin birni da kewaye kuma Sarkin Kudun Zazzau wanda Malam Nuhu ya wakilta, ya yaba wa gidauniyar a kokarin da suke yi wajen baiwa marayu kulawa ta fannin ilimi da lafiyar su da kuma koya masu sana’o’i.

Ya kara da cewa, zasu bada tasu gudummuwar don muhimmancin taimakon maraya.

Da yake nasiha a wurin taron, Mal. Bashir Abubakar Magaji Basharata, ya bayyana ko wane ne maraya da muhimmancin taimaka masa. Kuma ya yi fatan al’umma za su dukufa wurin taimakon marayu.

Wasu daga cikin marayun sun koka na rashin iyaye da zasu kula da matsalan su, sunce yanzu sun sami saukin hakan, tunda sun sami wannan gidauniya, inda suka godewa wadanda suke taimaka masu a fannoni da dama don inganta rayuwar su.

Da take jawabin godiya a madadin wadanda aka karrama, Mal. Halima Aliyu kofar Doka, ta gode wa gidauniyar tare da alkawarin cigaba da taimakawa gidauniyar a kowa ni lokaci.

Taron dai ya sami halartan shuwagabannin al-umma, ‘yan kungiyoyi maza da mata daga sassan Jihar Kaduna.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog