0
A ranar Alhamis, Allah Ya yi wa Alhaji Musa Sale Kwankwaso, tsohon Maji dadin Kano kuma sabon Makaman Karaye rasuwa a gidansa dake karamar hukumar Madobi a jihar Kano.
Basaraken shi ne mahaifin tsohon gwamnan Kano kuma tsohon Sanatan Kano ta tsakiya, Engr Rabi’u Musa Kwankwaso.
Ya rasu yana da shekara 93 a duniya. Kafin rasuwarsa ya kasance mai rike da sarautar Majidadin Kano kafin a rarraba Masarautar Kano gida 5.
Bayan rarrabawar da gwamnatin Kano ta yi, Majidadi ya fada Masarautar Karaye in da daga bisani aka daga darajar sarautar zuwa mai nadin Sarkin Karaye.
