Dan wasa Eden Hazard, dan kasar Belgium, ya bayyana cewa yaso bugawa Real Madrid kwallo tin lokacin yana karami.
Dan wasan ya bayyana haka ne a wani sakon bakwananshi bari kungiyarshi ta Chelsea zuwa Real Madrid.
Hazard ya wallafa sakon a shafinanshi na sada zumunta, inda ya bayyana godiyarshi ga magoya bayan kungiyar da suka nuna masa goyon baya a tsawon shekaru 7-8 da yayi yana taka leda a kungiyar ta Chelsea.
Ya kuma godewa mahukunta da ma’aikatan kungiyar gaba ki daya.