An shawo kan rashin jituwar Ganduje da Sarki Kano Sunusi

DaboFM ta binciko hakan na zuwa ne jim kadan bayan cimma matsaya tsakaninsu a daren Juma’a a babban birnin tarayyar Abuja.

Tin dai wunin Juma’a, jaridar Daily Nigerian ta rawaito cewa, Shugaba Buhari ya shiga tsakanin manyan mutanen guda 2, bayan da akayi ta cece kuce akan rashin shigar shugaba Buhari da sauran manyan Arewa cikin maganar.

Shiga tsakani da shugaba Buhari yayk na zuwa ne lokacin daya rage kwana 1 wa’adin da gwamnatin jihar ta bawa Sarkin Kano yayi jawabi akan batun almuzzaranci da kudin masarautar Kano.

DABO FM ta gane cewa “A lokacin ganawar da aka gudanar a daren Juma’a a garin Abuja, gwamnan tare da mai martaba sarki sun aminta da kawo karshen dambarwar domin saka lamuran jihar da mutanenta a gaba.

Duk da babu cikakken bayani game da ganawar, majiya daga fadar gwamnatin tarayya ta shaidawa Jaridar Daily Nigerian cewa shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya da gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi ne suka jagoranci ganawar tare da wasu manyan mutane.

“Abinda zan iya cewa shine ganawar ta haifar da ‘da mai ido. Dukkaninsu sun aminta da su zama tsintsiya mai madauri daya domin zaman lafiya da cigaban jihar Kano.” Kamar yadda majiyar ta tabbatar.

“Mun godewa Allah, yanzu dambarwar tsakanin gwamnan da Sarkin ta kare, za’a bawa shugaban kasa rahotan cigaban da aka samu.”

DABO FM ta tattaro daga DAILY NIGERIAN cewa duk da shawo kan matsalar, Sarkin Kano Muhammadu Sunusi II, yace lallai zai bada amsar da gwamnatin jihar ta bukata akan almubazzaranci da kudin masarautar.

Rikici tsakanin Gwamna Ganduje da Sarki Muhammadu Sunusi yayi tsamarine a dai dai lokacin da aka gudanar da zaben gwamnonin Najeriya.

Inda tsagin gwamnati ya zargi Sarki da marawa dan takarar PDP, Abba Kabir Yusuf baya a matsayin gwamnan jihar Kano.

%d bloggers like this: