Hon Muhammdu Gudaji Kazaure, dan majalissar Tarayya mai wakiltar karamar hukumar Gwiwa, Roni, Kazaure da ‘Yan kwashi, ya bayyana lashe zaben da ‘yayan jami’iyyar APC tayi a majalissar kwatankwacin irin bugun tazarar da Cristiano Ronaldo yaci a gasar cin kofin duniya ta 2018.