Bulaliyar majalissar dattijai, Sanata Orji Uzor Kalu na jihar Abia, ya bayyana cewa wasu daga cikin Sanatoci sun shiga cikin yi masa korafi akan albashin da aka basu a watan Yuni.
Sanata Orji yace; Sanatocin sunce ba haka sukayi tsammani za’a basu ba kafin zabe.
Gidan Talabijin na OAK TV ya rawaito cewa Sanata Orji ya bayyana haka ne a babban birnin tarayyar Abuja ya kuma bada tabbacin nan bada dadewa ba zai fito ya bayyana ainahin abinda Sanatocin suke samu.
Orji yace albashin da kafafen yada labarai suke rubutawa ana baiwa Sanatocin ba gaskiya bane inda ya bayyana cewa abinda ya karba a watan Yuni yayi kasa da abinda aka saba rawaito wa.
“Abunda kuke kira albashi mai tsoka sune kudaden da muke amfani da shi wajen gudanar da ayyuka a mazaba saboda basu bamu karin kudade. Kudin ne muke amfani da shi idan zamu yi tafiya zuwa Abia, Legas, ko Kaduna.”
Zuwa nan gaba zan bayyana muku, zaku ga cewa korafin da akeyi a kan yan Majalisar Dattawa suna karbar kudade na banza ne.”
A baya bayan nan ne dai manyan jaridun kasa suka rawaici albashi da alawus na Naira miliyan 14,330,000 da kowanne Sanata a Najeriya yake karba a kowanne wata.
Shima tsohon Sanata da ya fito daga jihar Kaduna, Shehu Sani ya bayyana hakikanin kudaden da ake baiwa kowanne sanata a wata wanda ya bada tabbacin abinda jaridun kasa suka fada gaskiya ne.
