Tue. Nov 19th, 2019

Dabo FM Online

World’s First pure Hausa online Radio

Kotu ta ki amincewa da bukatar ‘Abba Gida Gida’ na karin sunayen shaidu guda 8

1 min read

Kotun karbar korafe korafen zaman gwamnan jihar Kano dake da zamanta a jihar Kano tayi watsi da bukatar jami’iyyar PDP da dan takarar ta, Abba Kabir Yusuf.

PDP ta hannun lauyanta, Adegboyega Awomolo SAN, ya bukaci kotu da ta basu damar kara sunayen wasu guda 8, kari akan wanda suka bayar tin farkon shigar da karar.

Lauyan PDP, Awomolo , ya karyata rahotannin wasu kafafen yada labarai na cewa PDP ta nemi bukatar gyaran wasu kura-kurai da ta tafka a lokacin bada hujjojinta na kalubalantar zaben gwamna Dr Abdullahi Ganduje.

Ya bayyana cewa; karin sunayen shaidu kawai suka bukata daga kotun kuma tayi watsi da bukatar.

A nata bangaren, mai shari’a Halima Muhammad, alkaliyar dake jan ragamar kwamitin alkalan da zasu yanke hukunci, tace kotun tayi watsi da bukatar ne bisa zuwan ta a kurarren lokacin da ya sabawa shari’a.

DABO FM ta rawaito cewa, mai shari’a Halima Muhammad ta dage cigaba da zaman har zuwa 22 ga watan Yulin 2019, inda a nan ne kotun zata fara zaman shari’ar babu dagewa har sai an yanke hukunci.

©2019 Dabo FM Online. Sponsored by Dabo Media Group | Newsphere by AF themes.