Home LabaraiAl’ummar Gama sun cigaba da koka wa kan ‘Rijiyoyin Inconclusive’ na Baba Ganduje

Al’ummar Gama sun cigaba da koka wa kan ‘Rijiyoyin Inconclusive’ na Baba Ganduje

by Dabo Online
0 comments

Tin bayan cin zaben gwamnan jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje, al’ummar yankin Gama na karamar hukumar Nassarawa suke kokawa kan rashin karasa rijiyoyin da gwamnatin jihar ta fara.

Ba wannan ne karon farko da al’ummar suke koka wa ba.

Sun koka kan cewa tin bayan da aka sanar da sakamakon zaben Ganduje, har yau basu kara ganin keyar wani da sunan karasa ayyukan ‘Inconclusive’ da aka fara a yankin ba.

Tin dai a lokacin mutane sune ganin dama an shirya yin aikin ne dan cimma manufar samun kuri’ar mutanen yankin bayan da hukumar INEC ta ayyana sake jefa kuri’a a yankin biyo bayan soke na farko da hukumar tayi.

DABO FM ta binciko cewa kusan dukkanin ayyukan da gwamnatin Ganduje tayi a wannan yanki bai yi karko ba tin a karon farko.

Bincike da nuna cewa hatta wadanda suka ci gajiyar aikin ido a lokacin, kusan mutane 30 daga cikinsu dukka a yanzu sun makance – A rahotan da Arewa Radio Kano suka tabbatar.

You may also like

-
00:00
00:00
Update Required Flash plugin
-
00:00
00:00