Labarai

Atiku da Mahaifanshi dukkansu ba ‘Yan Najeriya bane – Abba Kyari ya fada wa Kotu

Abba Kyari, shugaban ma’aikatan shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya fadawa kotun sauraren karar zabe cewa Atiku Abubakar, dan takarar shugabancin kasa a PDP, dan kasar Kamaru ne.

Kyari yace Atiku dan asalin kasar Kamaru na jini.

Kyari ya bayyana haka ne a gaban kotun ta hannun lauya Wole Olanipekun, SAN, mai kare Shugaban Kasa, ya bayyana cewa a garin Jada aka haifi Atiku Abubakar a shekarar 1946 a lokacin da garin yana mallakin arewacin Kamaru.

Ya kara da cewa an haifi Atiku a garin Jada kafin a rabe tsakanin Najeriya da Kamaru, inda sai bayan da akayi zabe don baiwa Najeriya garin Jada.

Lauyan ya kara da cewa; yanayin rayuwar mutanen kasar Kamaru itace dai irin wacce akeyi a garin Jada, tare da cewa dangin Atiku, da ya hada da mahaifi da kakaninshi cikakkun ‘yan kasar Kamaru ne.

Daga karshen lauyoyin APC da na Muhammadu Buhari suna neman kotu ta kori karar bisa kasancewar wanda ba ‘dan Najeriya ba yayi takarar shugabancin kasa.

Karin Labarai

Masu Alaka

Dukkanin wakilan jami’iyyu sun aminta da’a soke zabe na 2 da akayi a mazabar Gama – Umar Yakasai

Dabo Online

Malaman addinai da ‘Yan siyasa ne suka haddasa kashe-kashe a Najeriya – Buhari

Dabo Online

Buhari ya amince da daukar ma’aikata 774,000

Dabo Online

Kamfe: Shugaba Buhari ya taka rawa

Dabo Online

Halayyar Buhari ta gaskiya ta bayyana bayan darewarshi shugabancin Najeriya – Buba Galadima

Muhammad Isma’il Makama

Hanan Buhari ta kammala digiri da maki mafi daraja

Muhammad Isma’il Makama
UA-131299779-2