Shugaba Muhammadu Buhari ya ce tsohuwar gwamnatinshi ta ceto mutane miliyan 5 daga kangin matsanancin talauci.
An dai bayyana Najeriya a matsayin kasar da tafi kowacce kasa matalauta da talauci yayi musu katutu a duniya. Wanda kaso 33.1 na ‘yan kasar suna cikin matsanancin talauci.
Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana haka ne a wajen taron bude ayyukanyi ga matasa, wanda kungiyar ayyukanyi ta duniya ta gabatar wanda da aka gudanar a garin Abuja, ranar Alhamis.
Shugaba Buhari ya samu wakilinci babban sakataren gwamnatin, Mista Boss Mustapha; Yace gwamnatin ta fitar da mutane daga talaucin ne a karkashin shirin ta na N-SIP.
“A wannan lokacin yanzu, maganar rashin aikin ga matasa, ansamu cigaba sosai, gwamnati ta saka gabanta wajen tallafawa matasa ta hanyar samar musu da mazaunin da zai sama musu ayyukanyi da yacce zasu gina rayuwarsu.”
“Tin daga farko, wannan gwamnatin ta zuba jarinta akan gina mutane, kirkiro da shirin NSIP ya farfado da tattalin arziki a kasa tare da kawo sakamako mai kyau a kasa wajen karuwar yawan matasan da suke shiga makaranta da kirkirar ayyukan yi.”
Shugaba Buhari ya kara da cewa; shirin ya samarwa da ‘yan Najeriya damammaki masu kyau hadi da fidda su daga matsanancin talauci.
“Misali, a shekaru 3 da suka gabata, shirin ya samar da ayyukanyi miliyan 2, ya kuma fitar da mutane miliyan 5 daga kangin talauci.
