Farfesa Egwaikhide Umoudu, babban malami dake koyarwa a Makarantar Koyar da Tsaro ta Najeriya ‘NDA’ dake garin Kaduna, ya bayyana cewa gwamatin Najeriya bata ci nasara a yakin da takeyi na yakar cin hanci da rashawa ba, bisa dalilin cewa dukkan ‘yan Najeriya suna amfani da cin hanci da rashawar.
Malamin ya bayyana haka ne a ranar Alhamis, 29 ga Agusta, 2019, a wani jawabi da yayi a wajen taron Kaddamar da Lakca a kan Makarantar ‘NDA’ karo na 10.
Farfesan yace; “Cin Hanci da Rashawa ne yake makalar da cigaban Najeriya. Duk muna amfana da shi. Daukar wanda bai chanchanta aiki ba, shi ma cin hanci da rashawa ne.
“Duk wani dan Najeriya yana yin rashawa, Ilimin mu a lalace yake da rashawa, tsare-tsarenmu a lalace suke da rashawa, har addinanmu ma an cika su da rashawa, dokokin kasar suma a lalace suke da rashawa.”
“Yaki da cin hanci da rashawar ma an siyasantar dashi, ana amfani dashi wajen daukar fansa. Najeriya ta ci maki 27 bisa 100 a jerin kasashe 180 dake yaki da cin hanci da rashawa.
DABO FM ta rawaito Farfesa Egwaikhide , ya kara da cewa kasar ba za ta fita daga matsalolin dake damunta ba har sai da karkato da kudade bangaren Ilimi, saboda Ilimin zai zama gatan kasar a nan gaba.
“Ilimi shi ne kashin bayan cigaba. Dole yan Najeriya su karkata wajen samun Ilimi. Tsarin Ilimin Najeriya cike yake da kura-kurai wadanda suka dakile ingancin karatun kasar baki daya.”
