1
Kotun dake sauraron korafe-korafen zaben Gwamna dake da zamanta a jihar Kaduna, ta tabbatar da gwamnan jihar, Mallam Nasiru El-Rufai, a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar.
Hakan na zuwa ne bayan korar karar da dan takarar gwamna a jami’iyyar PDP, Isa Ashiru, ya shigar na kalubalantar nasarar Mallam Nasiru.
