0
Gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasiru El-Rufa’i, ya sanya danshi, Abubakar, a makarantar Firamare ta gwamnati.
Hakan na zuwa ne bayan da gwamnan yayi alkawarin sanya danshi a makarantar gwamnati idan ya cika shekaru 6 tin a lokacin yakin neman zabenshi da yayi. – Daily Nigerian ta tabbatar.
Hakan wani mataki ne na samun inganci tare da nagartar karatu a makarantun jihar.
Gwamnan ya bayyana sanya dan nashi a makarantar ne a shafinshi na Twitter inda yace;
“Yau Abubakar Saddiq El-Rufa’i ya zama dalibin aji Firamare na 1 a Kaduna Capital school.”
