Tue. Nov 19th, 2019

Dabo FM Online

World’s First pure Hausa online Radio

Ya kamata mutanen Kano su takawa Kwankwaso birki akan yawo da kwakwalwarsu da yake yi – Ali Baba

2 min read
Alibaba Agama lafiya

Alibaba Agama lafiya

Babban mai bawa gwamnan jihar Kano akan harkokin addinai, Hon S.A Ali Baba Agama Lafiya Fagge, ya bayyana cewa ikirarin da ake yiwa Kwankwaso na ‘Mai Takalmin Karfe’ duk karya ce.

Ali Baba ya wannan kalami ne yayin da yake tattauna da gidan Rediyon Rahama dake birnin Kano.

DABO FM ta binciko Ali Baba yanayin tsokaci akan gidauniyar da tsohon gwamnan Kano a kafa domin tara kudaden tallafawa matasa wajen yin karatu a kasashen waje.

Ya bayyana cewa Kwankwaso ya kafa gidauniyar ne domin amfani kanshi, inda ya kara da cewa ”daga yin wata biyu babu mulki, Kwankwaso har ka fara neman kudi a wajen talakawa?.”.

“Ya (Kwankwaso) bude kasuwa, ya bugo kati, a nawa ya bugo? yayi lissafin na nawa ya bugo da nawa za’a samu riba.”

“Mu munsan mutanen Kano a waye suke, idonsu a bude yake, babu wani wanda zai siyar musu da abinda basu gani ba, babu abin siyarwar amma ace musu gashinan na siyarwa ne kudai ku bada kudi.”

“Yawo da kwakwalwar mutanen Kano da Kwankwaso yakeyi, yakamata su taka masa birki.” Wallahi ina fadan wannan akan Kwankwaso sabida Allah.”

Ali Baba yayi kira ga al’umma Kano cewa kada fa su manta shine mutumin da abaya yake fitowa ya kare Kwankwaso, ya fadi maganar da sai yanzu ya gane shima shirme yakeyi.

©2019 Dabo FM Online. Sponsored by Dabo Media Group | Newsphere by AF themes.