Home LabaraiYa sanya ‘danshi a makarantar da ya kashe wa miliyan 195, ya dauki Malamai 42 na musamman, El-Rufa’i

Ya sanya ‘danshi a makarantar da ya kashe wa miliyan 195, ya dauki Malamai 42 na musamman, El-Rufa’i

by Dabo Online
0 comments

Da safiyar yau ne gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasiru El-Rufa’i, ya kai ‘danshi Abubakar, makarantar Firamare ta Capital School dake jihar.

Hakan na zuwa ne bayan da gwamnan ya alkaurata sanya ‘dan nashi a makarantar gwamnati da zarar ya cika shekaru 6 a duniya.

Sai dai DABO FM tayi waiwaye wajen dubo irin ayyuka da gwamnan yayi a makarantar a watanni 17 da suka gabata, kama daga inganta ajujuwa da kawo ingantattun Malamai masu kwarewa.

A ranar 13 ga watan Maris, 2018, Kwamishinan Ilimi na jihar a wancen lokaci, Ja’afaru Sani, ya tabbatar da mayar da malamai 42 da suke aikin wucin gadi a makarantar suka zama Malaman din-din-din.

Haka zalika, gwamnatin ta bayyana gyaran Makarantar akan kudi na Naira miliyan 195 domin mayar da ita cikin jerin Makarantun da suka fi kowanne a fadin Najeriya. – Daily Trust, PM News, SignalNG da Majalissar kula da ayyukan raya kasa ta jihar KDMobp sun tabbatar da haka.

Hakan ce tasa wasu suke alakanta gyaran makarantar duk a cikin shirin saka danshi domin yin karatu a ciki.

Hasalima dai Makarantun “Capital Schools”, ba makarantu ne irin na gama-gari ba, domin kuwa ‘dan talaka bazai iya karatu aciki ba saboda tsadar ta.

A wata hira da sashin Hausa na BBC yayi da shugaban Makarantar, ya bayyana kudin da kowanne yaro yake biya a matsayin kudin makaranta a kowacce shekara.

A halin yanzu, iyaye suna gagara ture ‘ya’yansu Makarantun da ake biyan N750 kacal.

A jihar Kano, akwai Makarantar ‘Kano Capital School, itama makarantace da ‘dan talaka baya iya shigarta domin tsadarta.

You may also like

-
00:00
00:00
Update Required Flash plugin
-
00:00
00:00