Labarai

N30 kacal Banki zai caji wanda ya cire N501,000 a asusun Banki -CBN

Babban bankin Najeriya, CBN, yayi karin haske a game da sabuwar dokar cajar wadanda suka saka ko cire kudi sama da N500,000 daga asusun banki a Najeriya.

Da kuma sama da Naira Miliyan 3 a asusun kamfanunuwa.

A makon da muke ciki dai babban bankin ya kakaba sabuwar dokar wacce ta fara tim ranar 17 ga watan Satumbar 2019, a yunkurin da bankin yace yanayi na rage amfani da takardar kudi.

Babban bankin ya bayyana cewa; Wanda ya sanya N501,000 a cikin asusu, banki zai dauki kaso 2 a cikin Naira dubu dayar data hau kai na adadin data kayyade kadai, wanda a lissafi ya kama N20.

Wanda kuma ya cire N501,000, bankin zai dauko kaso 3 na iya Naira dubun data hau kan N500,000, ma’a za’a caji N30 kacal.

Haka zalika suma masu asusun Kamfanunuwa.

Comment here