//
Tuesday, April 7

Jar Miya: Ma’aikata sun fara karbar albashin N30,000

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta fara biyan ma’aikata sabon albashin N30,000.

Sai dai bincike ya bayyana cewa ma’aikata masu mataki na 1 zuwa na 6 ne kadai suka fara cin moriyar karin albashin tin a watan Agusta.

Shugaban kungiyar ma’aikatan Najeriya, Lawrence Ameachi, shine ya sanar da haka a ranar Lahadi, 22 ga watan Satumba.

“Sun fada mana cewar sun fara biyan sabon Albashin. Mun kuma samu tabbaci daga ‘ya’yan kungiyar mu cewa an biyasu sabon Albashin a watan Agusta, sun kuma alkauranta biyan bashin da ake bi a watan Satumba.”

Sai dai tattaunawarmu ta cigaba da tsaida matsaya ta samu tsaiko, amma a zaman mu na karshe, mun bayyana zamuyi magana da ‘ya’yan kungiyarmu, wanda kun riga munyi.

Masu Alaƙa  Kungiyar Kwadago ta bawa gwamnan jihar Niger wa'adin kwana 21 akan biyan albashin N30,000

“Yanzu haka muna jiran ‘ya’yan kungiyar tamu ne don jin wana mataki suke ganin zamu dauka.”

Karin Labarai

Share.

About Author

Comments are closed.

%d bloggers like this:
DABO FM 2020