Home LabaraiKungiyar ‘Yan Jaridu ta mika Ta’aziyyar rashin Ma’aikacin NTA

Kungiyar ‘Yan Jaridu ta mika Ta’aziyyar rashin Ma’aikacin NTA

by Mu’azu A. Albarkawa
0 comments

An bayyana rashin Marigayi Malam Hashimu Adamu, Ma’aikacin Tashar Talabijin na Kasa NTA Zaria, a matsayin babbar rashi ba ga kafar yada labarai ta NTA ko iyalan sa ba, rashi ne ga al’umma baki daya.

Shugaban Kungiyar ‘Yan Jarida ta Kasa shiyyar Zaria Kwamared Bello Habib, ya bayyana hakan, sa’ilin da yake mika sakon ta’aziyyar sa, ga Iyalai ‘Yan uwa da kuma abokan arziki na Hashim Adamu.

Ya kwatanta shi, a matsayin mutum mai natsuwa da kame kai da kuma haba-haba tsakanin abokan aikin sa, musamman lokacin da yake gudanar da aiki.

Ya naimi sauran ‘Yan Jaridu, su yi koyi da halayyan sa domin samun rayuwa mai kyau kuma abun kwatance.

Daga nan, sai Shugaban Kungiyar ‘yan Jaridan, ya mika sakon ta’aziyyar sa a madadin Kungiyar shiyyar Zaria, ga iyalai, ‘yan uwa da kuma Hukumar Tashar Talabijin na Kasa NTA, kuma ya roki Allah Rahimin Sarki ya gafarta masa kura-kuren sa.

You may also like

-
00:00
00:00
Update Required Flash plugin
-
00:00
00:00