Labarai

Abba Gida Gida ko Dr Ganduje? Kotu ta ayyana Ranar Larabar 2 ga Oktoba domin yanke hukunci

Kotun dake sauraron kararrakin zaben gwamnan jihar Kano, ta bayyana ranar da zata kawo karshen karshen Shari’ar da aka kalubalanci nasarar gwamnan Kano, Dr Ganduje.

Kotun da mai shari’a Halima Shamaki, take jagoranta ta ayyana ranar 2 ga watan Oktobar 2019 a matsayin ranar da zata yanke hukunci.

Dan takarar jami’iyyar PDP, Abba Kabiru Yusuf ne dai ya shigar da karar inda yake kalubalantar bayyana Dr Ganduje a matsayin wanda ya lashe zaben.

A watan Satumba, dukkanin bangarorin 3, APC, INEC da PDP sun gama bayyanawa kotu dukkanin hujjoji da kariyarsu, inda daga nan Kotu tace zata sanya ranar da zata yanke hukuncin.

Tin da dari dai PDP tace dan takararta ne ya samu nasara a zaben farko wanda aka gudanar a watan 9 ga watan Maris, 2019.

Sai dai a bangaren APC da INEC, sun bukaci kotu tayi watsi da karar bisa rashin ingantattun hujjoji da PDP ta gabatar.

Karin Labarai

Masu Alaka

Kano: Kotun daukaka kara ta tabbatar wa Hon Shamsuddeen Dambazau na APC kujerarsa

Muhammad Isma’il Makama

Kotun zabe ta kara tabbatar da Dr Ganduje a matsayin gwamnan Kano

Dabo Online

APC ta sake rasa kujerar Sanata, PDP ta sake cin galaba

Dabo Online

APC ta sake rasa kujerar Sanata, PDP ta sake samu

Dabo Online

Kai Tsaye: Daga Kotun sauraren karar zaben shugaban Kasa

Rilwanu A. Shehu

Kotun koli ta tabbatar da kujerar gwamna ga Kauran Bauchi

Dabo Online
UA-131299779-2