Home LabaraiHon Shamsuddeen Dambazau ya raba gagarumin tallafi ga wanda iftila’i ya afkawa

Hon Shamsuddeen Dambazau ya raba gagarumin tallafi ga wanda iftila’i ya afkawa

by Muhammad Isma’il Makama
0 comments

Dan Majalisa mai wakiltar Takai da Sumaila a Jam’iyyar APC, Hon Shamsuddeen Dambazau ya raba gagarumin tallafi ga wadanda iftila’i ya afkawa a kananun hukumomin da yake wakilta.

A wata tattaunawa a kafafan yada labarai, Hon Shamsuddeen ya bayyana wa Dabo FM irin alkhairan da suka samar dama wanda suke a tafe a Takai da Sumaila.

“Akwai iftila’i daya sauka kan alummar takai da sumaila, munkai wannan kudiri majalisa don samarwa allummar mu abinda zai rage musu radadi.”

“Mun samar da buhun siminti 600, shinkafa buhu dari 300, masara buhu 300, bandir din kwano 700, bandir bandir na seeling, madara, milo da dai sauransu, abubuwa fiye da 18.”

“Mun samar wa wadanda suka wahalarta mana da ababen hawa don saukaka musu a yanayin rayuwa, motoci, babura ga matasa da tsofaffi harda mace a ciki.”

“A kowanne wata akwai daliban mu da suke karatu suna fuskantar kalubale ta wajen biyan kudin makarantu saboda haka muna basu tallafin dubu 20, 30, 50.”

“Akwai matsalar matsuguni, wasu basu da matsiguni idan suka je makaranta, kwanan nan muka kamawa daliban mu matsuguni a wudil, wanda muka samar musu da gidan da zasu zauna domin yin karatun su cikin nutsuwa da kwanciyar hankali.”

“Akwai wasu ma daliban mu da suke neman matsuguni a kusa da makarantun su muna nan muna kokarin samar musu a kabuga.”

“Marasa lafiya masu ciwon koda muna bada kudin wankin koda da magunguna dubu 50, 70 da sauransu, idan akayi haihuwa muna taimakawa, da dai abubuwa na yau da kullum.”

“Akwai aikin samar da ruwansha a sumaila dama abubuwan da bazasu lissafu ba”

You may also like

-
00:00
00:00
Update Required Flash plugin
-
00:00
00:00