Home LabaraiKotu ta bayar da umarnin tisa keyar Sheikh Ibrahimul Zakzaky zuwa gidan gyaran halaye

Kotu ta bayar da umarnin tisa keyar Sheikh Ibrahimul Zakzaky zuwa gidan gyaran halaye

by Dabo Online
0 comments

Wata babbar kotu dake da zamanta a jihar Kaduna ta bayar da umarnin tisa keyar shugaban kungiyar Dan Uwa Musulmi ta Shi’a daga ofishin hukumar DSS zuwa gidan gyaran halaye.

Gidan Talabijin na Channels ya tabbatar da; “Alkalin ya bayyana cewa a mayar da Sheikh Zazzaky gidan gyara halin jihar Kaduna.”

Da yake yanke hukuncin, mai shari’a, Gideon Kudafa, yace mayar da Sheikh Zakzaky da mai dakinshi gidan gyaran halaye zai taimaka wajen baiwa Likitoci da Lauyoyinsu damar ganinsu.

You may also like

-
00:00
00:00
Update Required Flash plugin
-
00:00
00:00