//

Kasa da awanni 24 da yin tataburza, Majalissar Kano ta aminta da kudirin Ganduje na karin masarautu 4

0

Majalissar dokokin jihar Kano ta amince da yin dokar da zata bawa gwamnatin Kano damar kirkirar sabbin Masarautu 4 a jihar.

Gwamnan jihar Kano, Dr Ganduje ya aike da kudirin ne a ranar Litinin, wanda ya samu amintar ‘yan Majalissun a yau Alhamis.

DABO FM ta rawaito a jiya Laraba an samu tataburza tsakanin ‘yan Majalissar wanda daga jikinsu suka ki amincewa da wasu batutuwa da suka ce gwamnan ya baiwa kanshi iko dayawa a sha’anin Masarautar.

Hakan yasa Majalissar ta dage zamanta zuwa yau Alhamis domin cigaba da muhawara akan dokar.

DABO FM ta tattara cewa dokar ta samu amintar Majalissar, sai dai tayi gyara akan ikon da gwamna ya bawa kanshi na karawa da ragewa kowanne Sarki daraja a duk lokacin da yaso.

Masu Alaƙa  Kotu ta sake dakatar da Ganduje akan kirkirar sabuwar Majalissar Sarkunan Kano

Majalissar tace gwamnan zai iya yin hakan ne kadai idan ya kawo bukatar zuwa gaban domin neman sahalewarta,

Karin Labarai

Share.

About Author

Comments are closed.

%d bloggers like this:
©Dabo FM 2020