Home LabaraiMa’aikatar wutar lantarki ta kasa na shirin kara tsunduma yajin aiki

Ma’aikatar wutar lantarki ta kasa na shirin kara tsunduma yajin aiki

by Muhammad Isma’il Makama
0 comments

Akwai yiwuwar duhu ya karade Najeriya nan gaba, inda mu ka samu labarin cewa kungiyar NUEE ta Ma’aikatan wutan lantarkin kasar nan su na barazanar shiga yajin aiki.

Rahoton mu na nan Dabo FM ya bayyana cewa, ‘Ya ‘yan wannan kungiya sun fara nuna cewa za su iya cigaba da yajin aikin da su ka fara kwanaki, kamar yadda jaridar Legit.ng ta fitar.

Dama can an dakatar da yajin ne domin gwamnati ta saurare kukansu. A Ranar 23 ga Disamban 2019, mu ka samu rahoto cewa idan har gwamnatin Najeriya ta gaza cika alkawuran da aka yi da ita, Ma’aikatan wutar lantarkin za su koma yajin aikin.

Wannan kungiya ta na kukan cewa hukumar BPE ta ki biyan sama da tsofaffin Ma’aikatan wuta 2, 000 da aka sallama daga kamfanin PHCN aiki kudinsu, tun cikin shekarar 2013.

Haka zalika wannan kungiya ta na korafin cewa hukumar BPE ta Najeriya ta karbe makarantun da ta gina, ta mikawa wadanda su ka zuba kudinsu a kamfanonin wutan kasar.

You may also like

-
00:00
00:00
Update Required Flash plugin
-
00:00
00:00